1. Waɗannan su ne ka'idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka.
2. Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa.
3. Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,
4. da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama wadda za a cire tare da ƙodojin.