11. Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwa Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan.
12. Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi.
13. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
14. “Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu.
15. Sa'an nan ka faɗa wa Isra'ilawa, cewa, duk wanda ya saɓi Allah zai ɗauki alhakin zunubinsa,
16. za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.
17. “Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi.
18. Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.