L. Fir 23:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji.

6. Sa'an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai.

7. Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba.

8. A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.

9. Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

10. lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu.

11. Firist ɗin zai kaɗa damin hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, don a karɓe su. Firist zai kaɗa hadayar a kashegarin Asabar.

L. Fir 23