7. Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.
8. Kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka,
9. amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.
10. Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a.