18. Sauran man kuma da ya ragu cikin tafin hannunsa, firist ɗin zai shafa a kan wanda za a tsarkake. Firist zai yi kafara dominsa gaban Ubangiji.
19. Sai firist ya miƙa hadaya don zunubi domin ya yi kafara, don rashin tsarkin mutumin. Daga baya ya yanka hadaya ta ƙonawa.
20. Firist kuma zai miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a bisa bagaden. Da haka zai yi kafara dominsa, shi kuwa zai tsarkaka.
21. Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai,
22. da kuma kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa.
23. A rana ta takwas zai kawo su wurin firist don tsarkakewarsa a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji.
24. Sai firist ya ɗauki ɗan rago da man zaitun, ya miƙa su hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.
25. Sa'an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama.
26. Firist ɗin kuma zai ɗibi man ya zuba cikin tafin hannunsa na hagu.