Kol 3:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah.

2. Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke Sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba.

3. Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.

4. Sa'ad da Almasihu wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi a cikin ɗaukaka.

Kol 3