Kol 2:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Idan mutuwarku tare da Almasihu ta 'yanta ku daga al'adun duniyar nan, me ya sa kuke zama har yanzu kamar ku na duniya ne? Don me kuke bin dokokin da aka yi bisa ga umarnin 'yan adam da koyarwarsu,

21. kamar su, “Kada ka kama, kada ka ɗanɗana, kada ka taɓa”?

22. (Wato, ana nufin abubuwan da, in an ci su sukan ruɓa duka).

Kol 2