Kol 1:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,

5. saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,

6. wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.

7. Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,

Kol 1