K. Mag 6:32-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Amma mazinaci marar hankali ne, gama hallaka kansa yake yi.

33. Zai sha dūka, a wulakanta shi, zai dawwama cikin kunya.

34. Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama.

35. Ba zai karɓi biya ba, ba kyautar da za a yi masa wadda za ta kwantar da fushinsa.

K. Mag 6