K. Mag 30:2-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Hakika wautata ta sa na zama kamar dabba ba mutum ba,Ba ni kuwa da fahimi irin na mutum.

3. Ban koyi hikima ba,Ban kuwa san kome game da Allah ba.

4. Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko?Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa?Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa?Wa kuma ya kafa iyakar duniya?Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa?Hakika ka sani!

21-23. Akwai abu uku, i, har huɗu ma waɗanda duniya ba ta jurewa da su, watobara da ya zama sarki,wawa da ya ƙoshi da abinci,mummunar mace da ta sami miji,baiwar da ta gāji uwargijiyarta.

24-28. Akwai ƙananan abubuwa huɗu a duniya, amma suna da hikima ƙwarai, watotururuwa talikai ne marasa ƙarfi, amma duk da haka sukan tanadi abincinsu da rani,remaye ba ƙarfafa ba ne, duk da haka suna yi wa kansu gidaje a cikin duwatsu,fara ba su da sarki, amma duk da haka suna tafiya sahu-sahu.ƙadangare ma wanda ka iya kama shi a hannu, amma yana zama a cikin fādodin sarakuna.

29-31. Akwai abu uku, i, har huɗu ma da suke da kwarjini da taƙama a tafiyarsu, watoZaki wanda ya fi dukan dabbobi ƙarfi, ba ya ratse wa kowa daga cikinsu,bunsuru da zakara mai taƙama,sarkin da yake tafiya gaban jama'arsa.

K. Mag 30