4. Ka tace azurfa, gwani kuwa zai yi wani kyakkyawan abu da ita.
5. A kawar da mugayen mashawarta daga gaban sarki, hukumarsa za ta shahara a kan adalci.
6. Sa'ad da kake tsaye a gaban sarki, kada ka nuna kai wani abu ne, kana kai kanka inda Allah bai kai ka ba.
7. Gara a roƙe ka ka hau zuwa babban matsayi, da a faɗa maka ka ba da wurin da kake ga wanda ya fi ka maƙami.
8. Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi?
9. Idan kai da maƙwabcinka kun saɓa, ku daidaita a tsakaninku, kada a tona asiri.