K. Mag 23:29-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Wa ake yi wa kaito? Wa yake da baƙin ciki? Wane ne mafaɗaci? Wa yake yin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido?

30. Sai riƙaƙƙen mashayi wanda yake gaurayar ruwan inabi.

31. Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da yake ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa'ad da kake motsa shi.

32. Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka.

33. Idanunka za su riƙa gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka faɗi magana sosai ba.

34. Za ka ji kamar kana can cikin teku, jirin teku na ɗibarka kana lilo a kan rufin jirgin ruwa da yake tangaɗi.

35. Za ka ce, “Lalle an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in ƙara sha.”

K. Mag 23