K. Mag 21:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.

14. Kyauta a asirce takan kwantar da zuciyar wanda yake fushi da kai.

15. Sa'ad da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi baƙin ciki.

16. Mutuwa tana jiran wanda ya ƙi bin hanyar hankali.

K. Mag 21