K. Mag 21:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ne yake mallakar tunanin sarki a sawwaƙe kamar yadda yake yi da ruwan rafi.

2. Ko da a ce dukan abin da kake yi daidai ne, ka tuna fa Ubangiji ya san manufarka.

3. Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.

K. Mag 21