K. Mag 20:21-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.

22. Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.

23. Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma'aunin algus.

24. Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai?

K. Mag 20