K. Mag 20:17-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.

18. Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.

19. Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.

K. Mag 20