1. Gara a ci ƙanzo da rai a kwance, da gida cike da liyafa, amma cike da tashin hankali.
2. Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon.
3. Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.