K. Mag 16:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.

11. Ubangiji yana son ma'aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai.

12. Sarakuna ba za su iya jurewa da mugunta ba, gama adalci yake sa hukuma ta yi ƙarfi.

13. Sarki yana so ya ji gaskiya, zai kuwa ƙaunaci mutanen da suke faɗar gaskiya.

14. Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.

15. Alherin sarki kamar gizagizai ne masu kawo ruwan sama a lokacin bazara, akwai rai a ciki.

16. Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.

17. Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.

K. Mag 16