1. Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce.
2. Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji yana auna manufarka.
3. Ka roƙi Ubangiji, ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.
4. Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce.
5. Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.