K. Mag 14:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.

25. Sa'ad da mashaidi ya faɗi gaskiya zai ceci rayuka, amma maƙaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa'ad da ya faɗi ƙarairayi.

26. Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.

K. Mag 14