K. Mag 12:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutumin da yake ƙaunar ilimi yakan so a faɗa masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ƙi yarda a faɗa masa laifinsa.

2. Ubangiji yana murna da mutanen kirki, amma yakan hukunta masu shirya mugunta.

3. Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram.

K. Mag 12