K. Mag 10:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani.

21. Kalmomin mutumin kirki za su amfani mutane da yawa, amma kana iya hallaka kanka da wauta.

22. Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.

K. Mag 10