1. Karin maganar Sulemanu, ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila.
2. Ga Karin magana da za su taimake ka ka rarrabe da hikima, da kyakkyawar shawara, da fahimtar ma'anar zurfafan karin magana,
3. da yadda za ka karɓi koyarwa ta hanyar hikima, da adalci, da gaskiya, da sanin abin da yake daidai.