Josh 22:33-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Mutanen Isra'ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra'ubainawa da Gadawa suke zaune ba.

34. Ra'ubainawa da Gadawa suka sa wa bagaden suna Shaida, domin in ji su, “Shi shaida ne a tsakaninmu, cewa Ubangiji shi ne Allah.”

Josh 22