Josh 11:8-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.

9. Joshuwa kuwa ya yi musu kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, ya daddatse agaran dawakansu, ya kuma ƙone karusansu.

10. A wannan lokaci Joshuwa ya koma da baya ya ci Hazor, ya kashe sarkinta da takobi, gama a lokacin Hazor ita ce masarautar mulkokin nan.

11. Suka kashe dukan waɗanda suke cikinta da takobi, suka hallakar da su ƙaƙaf, ba wanda ya ragu. Joshuwa kuwa ya ƙone Hazor.

12. Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.

13. Amma mutanen Isra'ila ba su ƙone ko ɗaya daga cikin biranen da suke bisa tuddai ba, sai Hazor kaɗai Joshuwa ya ƙone.

14. Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba.

15. Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.

Josh 11