Josh 11:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba.

15. Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.

16. Ta haka kuwa Joshuwa ya ci ƙasan nan duka, da ƙasar tuddai, da Negeb duka, da dukan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Araba, da ƙasar tuddai ta Isra'ila da filayen kwarinta,

17. tun daga Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa wajen Seyir, har zuwa Ba'al-gad a kwarin Lebanon, a gindin Dutsen Harmon. Ya kama sarakunan wuraren nan, ya buge su ya kashe su.

18. Joshuwa ya daɗe yana yaƙi da su.

19. Ba wani birnin da ya yi amana da Isra'ilawa, sai dai Hiwiyawa da suke zaune a Gibeyon. Saura duka kuwa, an ci su da yaƙi.

20. Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra'ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Josh 11