Josh 10:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'an nan Joshuwa ya koma zango a Gilgal tare da dukan Isra'ilawa.

16. Waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.

17. Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.”

Josh 10