12. Joshuwa kuma ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa,
13. “Ku tuna da maganar da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku da ita, ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai hutar da ku, zai kuma ba ku wannan ƙasa.’
14. Da matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobinku, za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a wannan hayin Urdun, amma jarumawanku su haye tare da 'yan'uwanku da shirin yaƙi domin su taimake su,
15. har lokacin da Ubangiji ya hutar da 'yan'uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa'an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.”