9. Dukan jama'ar Isra'ila, duk wanda yake zaune a birnin Samariya, zai sani Ubangiji ne ya aikata haka. Yanzu suna da girmankai suna fāriya. Sun ce,
10. “Gine-ginen da aka yi da tubali sun rushe, amma za mu sāke gina su da dutse. An sassare ginshiƙan da aka yi da itacen durumi, amma za mu sāke kakkafa su da kyawawan itatuwan al'ul.”
11. Ubangiji ya kuta maƙiyansu daga Rezin su fāɗa su da yaƙi.
12. Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra'ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
13. Jama'ar Isra'ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba.
14. A rana ɗaya Ubangiji zai hukunta shugabannin Isra'ila da jama'arta. Zai hallaka kawunansu da ƙafafunsu, da dabino da iwa,
15. wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi!
16. Su waɗanda suke bi da jama'an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.