Ish 9:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ga shi, an haifa mana ɗa!Mun sami yaro!Shi zai zama Mai Mulkinmu.Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,”“Allah Maɗaukaki,”“Uba Madawwami,”“Sarkin Salama.”

7. Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba,Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin,Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa,Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.

8. Ubangiji ya hurta hukunci a kan mulkin Isra'ila, da a kan zuriyar Yakubu.

9. Dukan jama'ar Isra'ila, duk wanda yake zaune a birnin Samariya, zai sani Ubangiji ne ya aikata haka. Yanzu suna da girmankai suna fāriya. Sun ce,

10. “Gine-ginen da aka yi da tubali sun rushe, amma za mu sāke gina su da dutse. An sassare ginshiƙan da aka yi da itacen durumi, amma za mu sāke kakkafa su da kyawawan itatuwan al'ul.”

11. Ubangiji ya kuta maƙiyansu daga Rezin su fāɗa su da yaƙi.

12. Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra'ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

13. Jama'ar Isra'ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba.

Ish 9