15. Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su.
16. Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.
17. Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama.
18. Na san tunaninsu da ayyukansu. Ina zuwa domin in tattara jama'ar dukan al'ummai. Sa'ad da suka tattaru, za su ga abin da ikona zai yi,