15. Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu.
16. Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakonmu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe.
17. Don me ka bari muka ɓata daga al'amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.
18. Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.
19. Mun zama kamar ba ka taɓa zama mai mulkinmu ba, kamar mu kuma ba mu taɓa zama mutanenka ba.