1. Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana,Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!
2. Duhu zai rufe sauran al'umma,Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki,Daukakarsa za ta kasance tare da ke!
3. Za a jawo al'ummai zuwa ga haskenki,Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.
4. Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!'Ya'yanki maza za su taho daga nesa,Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.
5. Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki,Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi.Za a kawo miki dukiyar al'ummai,Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.