Ish 60:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana,Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!

2. Duhu zai rufe sauran al'umma,Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki,Daukakarsa za ta kasance tare da ke!

3. Za a jawo al'ummai zuwa ga haskenki,Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

4. Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!'Ya'yanki maza za su taho daga nesa,Za a É—auki 'ya'yanki mata kamar yara.

Ish 60