Ish 58:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce, “Ku yi kuka da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa! Ku ta da muryoyinku kamar busar ƙaho. Ku shaida wa jama'ata laifinsu, ku shaida wa zuriyar Yakubu zunubansu.

2. Duk da haka suna ta nemana kowace rana, suna murna su san al'amurana, sai ka ce su al'umma ce wadda take aikata adalci, wadda kuma ba ta rabu da dokokin Allahnta ba. Suna roƙona in yi musu shari'ar adalci, suna murna su zo kusa da Allah.”

3. Mutane sukan ce, “Me ya sa muka yi azumi, Ubangiji bai gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, Ubangiji kuwa bai kula ba?”Ubangiji ya ce musu, “Duba, a ranar da kuke azumi, nishaɗin kanku kuke nema, kuna zaluntar dukan ma'aikatanku.

4. Duba, kuna azumi don ku yi jayayya ne, ku yi ta faɗa, ku yi ta naushin juna. Irin wannan azumi naku a wannan rana, ba zai sa a ji muryarku a can Sama ba.

Ish 58