Ish 55:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai,Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.

5. Yanzu kuwa za ku kira al'ummai, baƙi,Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya,Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku!Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Zan sa dukan wannan ya faru,Zan ba ku girma da daraja.”

6. Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi,Yanzu da yake kusa.

7. Bari mugaye su bar irin al'amuransu,Su sāke irin tunaninsu.Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu,Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.

8. Ubangiji ya ce,“Tunanina ba kamar irin naku ba ne,Al'amurana kuma dabam suke da naku.

Ish 55