Ish 54:5-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki,Sunansa Ubangiji Mai Runduna!Allah Mai Tsarki na Isra'ila mai fansarki ne,Shi ne mai mulkin dukan duniya!

6. Kina kama da amaryaWadda mijinta ya rabu da ita, tana baƙin ciki ƙwarai.Amma Ubangiji yana kiranki zuwa gare shi, ya ce,

7. “A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.

8. Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci,Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.”Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.

Ish 54