1. Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa.Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda murna.Yanzu za ki ƙara samun 'ya'ya fiye da naMatar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!
2. Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki!Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!