1. Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu?Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?
2. Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girmaKamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa.Ba shi da wani maƙami ko kyan ganinDa zai sa mu kula da shi.Ba wani abin da zai sa mu so shi,Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.