Ish 50:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Na tsiraita ga masu dūkana.Ban hana su sa'ad da suke zagina ba,Suna tsittsige gemuna,Suna tofa yau a fuskata.

7. Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba,Gama Ubangiji Allah yana taimakona.Na ƙarfafa kaina domin in jure da su.Na sani ba zan kunyata ba,

8. Gama Allah yana kusa,Zai tabbatar da ni, marar laifi ne,Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni?Bari mu je ɗakin shari'a tare!Bari ya kawo ƙararrakinsa!

9. Ubangiji kansa zai kāre ni,Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne?Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe,Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!

Ish 50