10. “Kin amince da kanki cikin muguntarki,Kina tsammani ba wanda yake ganinki.Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata,Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah,Ba mai kama da ni!’
11. Duk da haka bala'i zai auko miki,Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba,Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya,Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!
12. Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki,Kina amfani da su tun kina ƙarama.Watakila za su yi miki wani taimako,Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.