Ish 42:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Allah ya ce,“Na daɗe na yi shiru,Ban amsa wa jama'ata ba.Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu,Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.

15. Zan lalatar da tuddai da duwatsu,In kuma busar da ciyawa da itatuwa,Zan mai da kwaruruka inda akwai rafi hamada,In kuma busar da kududdufan ruwa.

16. “Zan yi wa mutanena makafi jagoraA hanyar da ba su taɓa bi ba.Zan sa duhunsu ya zama haske,In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu.Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.

17. Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka,Masu kiran siffofi allolinsu,Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”

18. Ubangiji ya ce,“Ku kasa kunne, ya ku kurame!Ku duba da kyau sosai, ku makafi!

19. Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta,Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?

20. Isra'ila, kun ga abu da yawa,Amma bai zama da ma'ana a gare ku ba ko kaɗan.Kuna da kunnuwan da za ku ji,Amma a ainihi me kuka ji?”

Ish 42