26. “Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.
27. Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.
28. “Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni.
29. Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”
30. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan.