Ish 33:8-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Manyan karauku suna da hatsari har ba mai iya binsu. Aka keta yarjejeniya, aka ta da sharuɗa. Ba a kuma ganin girman kowa.

9. Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.

10. Ubangiji ya ce wa al'ummai, “Yanzu zan tashi! Zan nuna irin ikon da nake da shi.

11. Kuka yi shirye-shiryen banza, kowane abu da kuke yi kuma ba shi da amfani. Kuna hallakar da kanku!

12. Za ku marmashe kamar duwatsun da aka ƙona don a yi farar ƙasa, kamar ƙayayuwan da aka ƙone suka zama toka.

13. Bari kowa da yake kusa da na nesa ya ji abin da na yi, ya kuma san ikona.”

14. Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”

15. Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa.

16. Sa'an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.

17. Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa.

18. Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare.

19. Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba!

20. Ku duba Sihiyona, birni inda muke idodinmu. Ku duba Urushalima! Za ta zama wurin zama mai lafiya! Za ta zama kamar alfarwar da ba ta taɓa gusawa ba, wadda ba a taɓa tumɓuke turakunta ba, igiyoyinta kuma ba su taɓa tsinkewa ba.

21. Ubangiji zai nuna mana ɗaukakarsa. Za mu zauna a gefen koguna da rafuffuka masu faɗi, amma ba kuwa jirgin ruwan abokan gāba da zai bi ta cikinsu.

24. Ba wanda zai zauna a ƙasarmu har ya ƙara yin kukan yana ciwo, za a kuma gafarta dukan zunubai.

Ish 33