Ish 26:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji,Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi,Waɗanda suke dogara gare ka.

4. Ku dogara ga Ubangiji har abada.Zai kiyaye mu kullayaumin.

5. Ya ƙasƙantar da masu girmankai,Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki,Ya rusa garunsa ƙasa.

6. Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu,Suna tattaka shi da ƙafafunsu.

7. Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul,Hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya,

8. Muna bin nufinka, muna sa zuciya gare ka.Kai kaɗai ne bukatarmu.

9. Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya.Sa'ad da kake yi wa duniya da jama'arta shari'aDukansu za su san yadda adalci yake.

Ish 26