Ish 26:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Rana tana zuwa da jama'a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza.Birni ƙaƙƙarfa ne,Allah kansa yake tsare garukansa!

2. A buɗe ƙofofin birnin,A bar amintacciyar al'umma ta shiga,Al'ummar da jama'arta take aikata abin da yake daidai.

3. Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji,Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi,Waɗanda suke dogara gare ka.

4. Ku dogara ga Ubangiji har abada.Zai kiyaye mu kullayaumin.

Ish 26