Ish 13:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.

8. Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.

9. Ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana ce ta zafin fushinsa. Za a mai da duniya jeji, a hallaka kowane mai zunubi.

10. Kowane tauraro, da kowace ƙungiyar taurari za su daina ba da haske. Rana za ta yi duhu lokacin da ta fito, wata kuwa ba zai ba da haske ba.

11. Ubangiji ya ce, “Zan kawo masifa a duniya. Zan hukunta dukan mugaye saboda zunubansu. Zan ƙasƙantar da kowane mai girmankai. Zan hukunta kowane mai izgili da mai mugunta.

12. Sauran da suka ragu za su fi zinariya wuyar samuwa.

13. Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa'ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.

Ish 13