Ish 13:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ba wanda zai ƙara zama a cikinta. Ba wani Balaraben da yake yawo da zai kafa alfarwarsa a can. Ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.

21. Za ta zama wurin zaman namomin jejin hamada, inda mujiyoyi za su yi sheƙarsu. Jiminai za su zauna a can, awakin jeji za su yi ta warnuwa a cikin kufanta.

22. A hasumiyarta da fādodinta za a ji amsar ihun koke-koken kuraye da na diloli. Lokacin Babila ya yi! Kwanakinta sun kusa ƙarewa!”

Ish 13