Ish 11:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Masarautar Isra'ila ba za ta ƙara jin kishin Yahuza ba, Yahuza kuma ba za ta zama abokiyar gābar Isra'ila ba.

14. Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama'ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya.

15. Ubangiji zai kawo iska mai zafi wadda za ta busar da Kogin Nilu, da na Yufiretis. Zai bar ƙananan rafuffuka bakwai ne kaɗai, don kowa da kowa ya taka ya haye.

16. Za a yi babbar karauka daga Assuriya domin sauran mutanen Isra'ila da suka ragu a can, kamar yadda aka yi wa kakanninsu sa'ad da suka bar Masar.

Ish 11