Ish 10:33-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Ubangiji Mai Runduna zai sa su ragargaje har ƙasa, kamar rassan da aka sassare daga itace. Masu girmankai da manyansu za a datse su ƙasa, a ƙasƙantar da su.

34. Ubangiji zai sassare su har ƙasa kamar yadda ake sassare itatuwa da gatari a tsakiyar kurmi, kamar yadda itatuwa mafi kyau na Lebanon za su fāɗi.

Ish 10